24 Oktoba 2021 - 20:37
​Sudan: Sojoji Sun Killace Gidan Kason Da Ake Tsare Da Albashir

Kafofin yada labaran Sudan sun ruwaito a yammacin jiya Asabar cewa, sojojin kasar sun dauki tsauraran matakan tsaro a daura da gidan kason Kober da ke babban birnin kasar Khartoum, inda hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir yake tsare.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da sanyin safiyar jiya Asabar ne wasu gungun masu zanga-zangar suka mamaye hedikwatar kamfanin dillancin labarai na Sudan "SUNA", gabanin wani taron manema labarai da aka shirya gudanarwa na wata tawaga ta "tawagar shelar 'yanci da sauyi".

Kafofin yada labaran cikin gida sun tabbatar da cewa, kimanin mutane 150 ne suka yi zaman dirshan a gaban fadar ta Republican.

Masu goyon bayan hukumomin sojin kasar ta Sudan ne suka aukawa masu zaman dirshan din, tare da hana gudanar da taron manema labarai, na kungiyoyi da jam’iyyun da ke neman a mika mulki ga hannun farar hula a kasar akasar.

342/